Tambaya ta 7. Waɗanne ne bukukuwan idi na Musulmai?

Amsa: Idin Karamar sallah, da kuma Idin Babbar sallah.

Kamar yadda ya zo acikin Hadisin Anas, ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya gabato Madina, alhali su suna da kwanaki biyu da suke wasa a cikinsu, sai ya ce: "Waɗanne kwanaki biyu ne waɗannan?", sai suka ce: Mun kasance muna wasa a cikin su ne a lokacin Jahiliyya, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai Allah Haƙiƙa Ya canza muku su da waɗanda suka fisu alheri, su ne: Ranar Babbar Sallah, da kuma Ranar Karamar Sallah". Abu Dawud ne ya ruwaito shi.

Dukkan wasu bukukuwan idin da ba su ba, to suna daga cikin bidi'o'i.