Amsa:
1. Algusu, dag cikin hakan akwai: Boye aibin haja (Abin sayarwa).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda dashi -, lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya wuce wani shuri - wato shuri - na abinci, sai ya shigar da hannunsa acikin sa, sai 'yan yatsun sa suka samu danshi, sai ya ce: " Menene wannan ya kai mai wannan abincin? Sai ya ce: Ai ruwan sama ne ya zuba acikin su ya Ma'aikin Allah, sai ya ce: "Shin ba ka sanya shi a saman abin cin ba, domin mutane su gan shi? Duk wanda ya yi mana algusu to baya tare da ni". Muslim ne ya ruwaito shi.
2. Riba: Daga cikinta in karɓi dubu ɗaya daga wani mutum bashi akan in dawo masa dasu da dubu biyu.
Karin, shi ne ribar da aka haramta.
Allah - Madaukakin sarki - Ya ce: "Kuma Allah Ya halatta ciniki kuma Ya haramta riba". [Surat Al-Baƙara: 275].
3. Ruɗu da Jahilta: Kamar in siyar maka da madara a hantsar akuya, ko kuma kifi acikin ruwa, alhali ban kamo shi ba.
(Ya zo) acikin Hadisi: "Manzon Allah - tsira da aminci Allah su tabbata a gare shi - yayi hani daga cinikin garari (Ruɗu). Muslim ne ya ruwaito shi.