Tambaya ta 13. Su waye maƙiyan mutum?

1. Rai mai umarni da mummnan aiki: Wannan shi ne mutum ya bi abinda ran shi yake riya masa da kuma san ran sa acikin saɓon Allah - mai girma da ɗaukaka -, tsarki ya tabbatar masa Ya ce: {Lalle rai mai umarnice da mummunan aiki, sai dai wanda Ubangijina Ya yi wa rahama, lalle Ubangiji na Mai yawan gafara ne kuma Mai yawan jinƙai ne}. [Surat Yusuf: 53]. 2. Shaiɗan. Shi ne maƙiyin ɗan Adam, babban manufarsa shi ne ya ɓatar da mutum, ya sanya masa waswasi na sharri, ya kuma shigar da shi wuta, Allah - Maɗaukakin sarki - ya ce: {Kuma kada ku bi hanyoyin shaiɗan, lallai cewa shi gareku maƙiyi ne mai bayyanar da ƙiyayya}. [Surat Al-Baƙarah: 168]. 3. Muggan abokai: Waɗanda suke kwaɗaitarwa akan sharri, kuma suna toshewa daga (aikata) alheri. Allah - Maɗaukakin sarki - yace: {Masõya a yinin nan, sãshensu zuwa ga sãshe maƙiya ne, fãce mãsu taƙawa (sũ kam mãsu son jũna ne)}. [Surat Al-Zukhruf: 67].