Tambaya ta 19. Me kake faɗa da safe da kuma yamma na zikirai?

Amsa. 1. Ina karanta Ayatul Kursiyyu: {Allah, bãbu wani abin bautawa da gaskiya fãce Shi, Rãyayye, Mai tsayuwa da kõme, gyangyaɗi bã ya kãma Shi, ballantana barci, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wane ne wanda yake yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa? Yana sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bãyansu. Kuma bã su kẽwayẽwa da kõme daga ilminSa, fãce da abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa. Kuma tsare su bã ya nauyayarSa. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma}. [Surat Al-Baƙara: 255]. 2. Ina kuma karanta: Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jin ƙai. 1. {Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci 1. Alla shi ne abun nufi da Buƙata 2. 3 Bai haifa ba kuma ba'a haife shi ba 3. 4. Kuma babu ɗaya da ya kasance kini a gare Shi 4}. Kafa uku. Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai. 1. {Ka ce "ina neman tsari ga Ubangijin safiya 1. Daga sharrin abin da Ya halitta 2. Daga sharrin dare, idan ya yi duhu 3. Daga sharrin mãtã mãsu tõfi a cikin kuduri 4. Daga sharrin mai hasada idan ya yi hasada 5}. Kafa uku. Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai. {Ka ce: "ina neman tsari ga Ubangijin mutane 1}. Mamallakin mutane 2. Ubangijin Mutane 3. Daga sharrin mai sanya wasuwãsi, mai ɓoyewa 4. Wanda ke sanya wasuwãsi a cikin ƙirãzan mutane 5. Daga Aljannu da mutane 6}. Kafa uku. 3. "Ya Allah kaine Ubangijina babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, Ka halicceni kuma nine bawan Ka, kuma ni ina kan alƙawarin Ka da wuyayen Ka iya iyawata, ina neman tsarin Ka daga sharrin abinda na aikata, ina iƙirari da ni'imar Ka gareni, kuma ina iƙirari da zunubi na, to ka gafarta mi ni, cewa shi ba mai gafarta zunubai sai Kai". Bukhari ne ya ruwaito shi.