Tambaya ta 9. Mece ce kishiyar gaskiya?

Amsa: Karya. Ita ce kuma saɓanin haƙiƙa, daga wannan: Yi wa mutane ƙarya, da saɓawa alƙawaruka, da shaidar ƙarya (zur).

Annabi - tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai ƙarya tana shiryarwa zuwa fajirci, kuma lallai fajirci yana shiryarwa zuwa wuta, lallai mutum zai dinga yin ƙarya har sai an rubuta shi cikakken maƙaryaci a wurin Allah". Anhaɗu akansa (Bukhari da Muslim suka rawaito shi). Annabi - tsira da aminci su tabbata agareshi - ya ce: ("Alamomin munafiki uku ne" sai ya ambata daga ciki: "Idan ya bada labari sai ya yi ƙarya, kuma idan ya yi alƙawari ya saɓa". Anhaɗu akansa (Bukhari da Muslim suka rawaito shi).