Tambaya ta 27. Mece ce ɓarna? kuma menene rowa? kuma menene karamci?

Amsa: Barna ita ce kashe dukiya ba tare da haƙƙinta ba.

Kishiyarsa: Rowa: Ita ce kamewa daga haƙƙinta.

Abinda yake daidai shi ne kasantuwa tsaka-tsakiya tsakaninsu, kuma musulmi ya kasance mai karamci ne.

Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma waɗanda suke idan sun ciyar, bã su yin ɓarna, kuma bã su yin ƙwauro, kuma (ciyarwarsu) sai ta kasance a tsakãnin wancan da tsakaitãwa}. [Suratul Furƙan: 67].