Amsa: 1. Fushi abin yabo: Shi ne kuwa ya kasance domin Allah, idan kafIrai ko munafukai ko wasun su suka keta alfarmar Allah - tsarki ya tabbatar masa -.
2. Fushi abin zargi: Shi ne fushin da zai sanya mutum ya aikata ko ya faɗi abinda baya kamata.
Maganin fushi abin zargi.
Yin alwala.
Zama, idan ya kasance a tsaye yake, da kuma kwanciya idan ya kasance a zaune yake.
Ya lazimci wasiyyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - acikin wannan: "Kada ka yi fushi".
Ya riƙe ran sa daga afkawa wani abu ayayin fushin.
Neman tsarin Allah daga Shaiɗan abin jefewa.
Yin shiru.