Amsa: Shi ne kada mutum ya ga kan sa (mafifici) akan mutane, kada ya wulaƙanta mutane, kada kuma yaƙi gaskiya.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma bayin Mai rahama su ne waɗanda suke tafiya a bayan ƙasa cikin sauƙi}. [Suratul Furƙan: 62]. Wato: Masu ƙanƙar da kai. Manzon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kuma wani ɗaya bazai ƙankar da kai ga Allah ba face sai Allah ya ɗaukaka shi". Muslim ne ya ruwaito shi. Manzon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai Allah ya yi wahayi zuwa gareni cewa ku ƙanƙar da kanku, ta yadda babu wani ɗaya da zai yi alfahari a kan wani ɗaya, kuma kada wani ɗaya ya yi zalinci akan wani ɗaya". Muslim ne ya ruwaito shi.