Tambaya ta 18. Menene Izgili?

Amsa: Shine izgili ga ɗan'uwan ka musulmi, da wulaƙantar da shi, wannan baya halatta.

Allah - maɗaukakin sarki - Ya ce dangane da hani daga hakan: {Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada waɗansu mutãne su yi izgili game da waɗansu mutãne, mai yiwuwa ne (abin yi wa izgilin) su kasance mafifita daga gare su (mãsu izgilin), kuma waɗansu mãtã kada su yi izgili game da waɗansu mãtã mai yiwuwa ne su kasance mafĩfĩta daga gare su. Kuma kada ku aibata kanku, kuma kada ku jẽfi jũna da miyãgun sunãye na laƙabõbĩ. Tir da sũna na fãsiƙanci a bãyãn ĩmãni. Kuma wanda bai tũba ba, to, waɗannan sũ ne azzãlumai 11}. [Suratul Hujurat: 11].