Tambaya ta 17. Mecece Hassada?

Amsa: Ita ce fatan gushewar ni'ima daga wani, ko kuma ƙyamar ni'ima ga wani.

Allah - maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma daga sharrin mai hassada idan ya yi hassada 5}. [Suratu Falaƙ: 5].

Daga Anas ɗan Malik - Allah ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada ku ƙi juna, kada ku yiwa juna hassada, kada ku juyawa juna baya, ku kasance - yaku bayin Allah - 'yan'uwan juna. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.