Amsa: Ita ce sakin fuska, tare da farin ciki da murmushi da tausasawa, da bayyanar da farin ciki a lokcin haɗuwa da mutane.
Ita ce kuma kishiyar ɗaure fuska a fuskar mutane daga abinda zai kore su.
Acikin falalaR hakan hadisai da yawa sun zo, daga Abu Zarr - Allah ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce da ni: "Kada ku wulaƙanta wani abu daga aikin alheri, koda kuwa ka haɗu da ɗan'uwan ka ne da sakakkiyar fuska". Muslim ne ya rawaito shi. Manzon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata agareshi - ya ce: "Murmushin ka a fuskar ɗan'uwan ka sadaka ne". Al-TirmiZi ne ya ruwaito shi.