Tambaya ta 8. Ka ambaci ladubban rashin lafiya, da kuma ziyarar marasa lafiya.

Amsa: 1. A lokacin da nake jin raɗaɗi, ina ɗora hannu na na dama a wurin sa, sai in ce: "Bismillah". Sau uku, sai kuma in ce: "Ina neman tsari da buwayar Allah da kuma ikoin sa (ya kare ni) daga sharrin abinda nake ji, kuma nake tsoro". Sau bakwai.

2. Ina yarda da abinda Allah ya ƙaddara shi, kuma ina haƙuri.

3. Ina gaggawar ziyartar ɗan uwa na mara lafiya, kuma ina ma sa addu'a, ba na tsawaita zama a wurin sa.

3. Ina masa addu'a ba tare da ya nema daga gareni ba.

5. Ina yi masa wasiyya da yin haƙuri da addu'a, da kuma sallah da tsarkaka gwargwadon yanda zai iya.

5.Addu'a ga maralafiya: "Ina roƙon Allah mai girma, Ubangijin Al'arshi maigirma da ya baka lafiya". Sau bakwai.