Tambaya ta 3. Ka ƙarasa Hadisin: "Wata rana mu muna zaune a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -..." kuma ka ambaci wasu daga fai'dojin sa.

Daga Umar ɗan Khaɗɗab - Allah ya yarda da shi - ya ce: “A yayin da muke zaune tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wata rana, yayin da wani mutum ya ɓullo mana, mai tsananin farin tufafi, mai tsananin baƙin gashi, ba a ganin alamun tafiya agare shi, kuma babu wani ɗaya daga cikin mu da ya san shi, har sai da ya zauna zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma ya sanya gwiwowin sa a gwiwoyin sa, ya sanya tafukan sa akan cinyoyin sa, sai ya ce: "Ya Muhammad, ka bani labari game da Musulunci? Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - ya ce: "Musulunci: Ka shaida cewa babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah, kuma lallai Muhammadu Manzon Allah ne, kuma ka tsayar da sallah, ka ba da zakka, ka Azumci Ramadan, kuma ka yi Hajjin ɗaki idan kasami ikon zuwa gare shi". Ya ce: "Ka yi gaskiya", sai mukayi mamakin sa, yana tambayar sa kuma yana gasgata shi. Yace: "To ka bani labari game da imani? Ya ce: "Ka bada gaskiya da Allah, da Mala'ikunsa, da littafan sa, da Manzannin sa, da Ranar Lahira, kuma ka yi imani da ƙaddara, alherin sa da sharrin sa. Ya ce: "Kayi gaskiya" Yace: "To kabani labari game da kyautatawa". Yace: "Ka bauta wa Allah kamar kana ganin sa, idan ka kasance ba ka ganin sa, to Shi yana ganin ka". Yace: "Ka bani labari game da Al-ƙiyama". Yace: "Wanda ake tambaya baifi wanda yake tambayar sani ba". Yace: "Ka bani labari game da alamomin ta". Yace: "Kuyanga ta haifi uwargijiyar ta, kuma kaga marasa takalma talakawa masu kiwon dabbobi, suna gasa acikin tsawaita gini'. Sannan ya tafi sai na zauna tsawon lokaci, sannan yace: "Ya Umar, shin kasan mai tambayar?" Na ce: "Allah da Manzonsa ne mafi sani" Yace: "Lallai shine Jibrilu, yazone dan ya sanar daku addinin ku". Muslim ne ya rawaito shi.

Abinda za'a iya koya daga Hadisin:

1. Ka ambaci rukunan Musulunci guda biyar, sune:

Shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Muhammadu Manzon Allah ne.

Da tsayar da sallah.

Da bayar da zakkah.

Da Azumin watan Ramadan.

Da Hajjin ɗakin Allah mai alfarma.

Ambaton rukunan Imani, su shida ne:

Imani da Allah.

Da Mala'ikun sa.

Da Littattafan sa.

Da Manzannin sa.

Da Ranar Lahira.

Da ƙaddara alherin sa da kuma sharrin sa.

3- Ambaton rukunan kyautatawa, shi rukuni ɗaya ne, shine, ka bauta wa Allah kamar kana ganin sa, idan ba ka kasance kana ganin sa ba to shi yana ganin ka.

4- Lokacin tashin Al-ƙiyama, babu wanda ya san shi sai Allah maɗaukakin sarki.

Hadisi na Huɗu: