Tambaya ta: 9. Ka ranta Suratl Kuraish? kuma ka fassara ta.

Amsa: Suratu Kuraishi da fassarar ta:

Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.

1. {Saboda sabon Kuraishawa 1. 2. Sabonsu na tafiyar hunturu da ta bazara 2. 3. Sabõda haka sai su bauta wa Ubangijin wannan Gida (Ka'abah) 3. 4. Wanda Ya ciyar da su (Ya hana su) daga yunwa, kuma Ya amintar da su daga wani tsõro 4. [Surat Kuraish: 1 - 4].

FASSARA:

1. {Sabon da Kuraishawa sukayi 1}: Abin nufi da wannan shine abinda suka kasance suna sabo da shi daga tafiya acikin hunturu da bazara.

2. {Sabonsu na tafiyar hunturu da ta bazara 2}: Tafiyar hunturu zuwa Yaman, da tafiyar bazara zuwa ƙasar Sham suna amintattu.

3. {Sabõda haka sai su bauta wa Ubangijin wannan Gida (Ka'abah) 3}: Sai su bautawa Ubangijin wannan ɗakin mai alfarma shi kaɗai, wanda ya sawwaƙe musu wannan tafiya, kada su haɗa shi da kowa wurin bauta.

4. {Wanda Ya ciyar da su (Ya hana su) daga yunwa, kuma Ya amintar da su daga wani tsõro 4}: Shi ne wanda Ya ciyar da su daga yunwa, kuma Ya amintar da su daga tsoro, na abin da Ya sanya azukatan Larabawa na girmama wannan Harami, da girmama mazauna wurin.