Tambaya ta: 8. Ka ranta Suratul Fil, kuma ka fassara ta.

Amsa- Suratul Fil da kuma fassararta:

Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.

1. {Ashe, ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata ga mutanen giwa ba 1? 2. Ashe, bai sanya kaidinsu a cikin ɓata ba 2? 3. Kuma Ya sako, a kansu, wasu tsuntsãye, jama'a-jama'a 3. 4. Suna jifar su da wasu duwatsu na yumɓun wuta 4. 5. Sa'an nan Ya sanya su kamar karmami wanda aka cinye 5. [Surat Al-Fil: 1 - 5].

FASSARA:

1. {Ashe, ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata ga mutanen giwa ba 1?} Ashe ba ka sani ba - ya kai wannan Manzo - yadda Ubangijin ka Ya yi da Abraha ba, shi da mutanan sa ma'abota giwaye,yayin da suka yi nufin rushe Ka'aba?

2. {Ashe, bai sanya kaidinsu a cikin ɓata ba 2?} Haƙiƙa Allah ya mayar da mummunan makircinsu na ruishe Ka'abah acikin tozarta, basu sami abinda sukayi buri na kawar da mutane daga Ka'aba, kuma ba su sami komai daga gare ta ba.

3. {Kuma Ya sako, a kansu, wasu tsuntsãye, jama'a-jama'a 3}: Kuma ya aika musu da tsuntsaye suka je musu jama'a jama'a.

4. {Suna jifar su da wasu duwatsu na yumɓun wuta 4}: Suna jifansu da duwatsu na taɓo masu tsananin zafi.

5. {Sa'an nan Ya sanya su kamar karmami wanda aka cinye 5}: Sai Allah Ya mayar da su kamar ganyan karmami da dabbobi suka cinye shi kuma suka take shi.