Tambaya ta: 7. Ka ranta Suratul Humaza, kuma ka fassara ta.

Amsa: Suratul Humaza da kuma fassararta:

Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.

1. {Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa) 1. 2. Wanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa 2. 3. Yana zaton cẽwa dũkiyarsa za ta dawwamar da shi 3. 4. A'aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama 4. 5. Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cẽ wa Huɗama 5? 6. Wutar Allah ce wadda ake hurawa 6. 7. Wadda take lẽƙãwa a kan zukata 7. 8. Lalle ne ita abar kullẽwa ce a kansu 8. 9. A cikin wasu ginshiƙai mĩƙaƙƙu 9}. [Surat Al-Humazah: 1 - 9].

FASSARA:

1. Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa) 1}: Azaba da tsananin azaba ta tabbata ga dukkan wanda yake yin gulmar mutane da suka acikin su.

2. {Wanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa 2}: Wanda shi himmar sa ita ce tara dukiya da lissafa ta, ba shi da wata himma in ba haka ba.

2. {Yana zatan cewa dukiyarsa zata dawwamar dashi 3}: Yana zatan cewa dukiyar sa wacce ya tarata zata tseratar da shi daga mutuwa, zai wanzu yana madawwami acikin rayuwar duniya.

4. (A'aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama 4}: Al'amarin ba kamar yadda wannan jahilin yake hasashe ba ne, tabbas sai an watsa shi a wutar Jahannama wacce take niƙe ta karya duk abinda aka watsa a cikinta saboda tsananin masifar ta.

5. Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cẽ wa Huɗama?Me ya sanar da kai - Ya kai wannan Manzo mai girma- mece ce wannan wutar wacce take haɗe duk abin da aka watsa cikinta?!

6. {Wutar Allah ce wadda ake hurawa 6}: Lallai cewa ita wutar Allah ce abar rurawa.

7. {Wadda take lẽƙãwa a kan zukata 7}: Wacce take zarcewa daga cikin jikkunan mutane zuwa zuciyoyin su.

8. {Lalle ne ita abar kullẽwa ce a kansu 8}: Ita abar kullewace akan waɗanda ake azabtarwa acikin ta.

9. {A cikin wasu ginshiƙai mĩƙaƙƙu 9}: Da wasu turaku miƙaƙƙu dogaye ta yadda bazasu iya fita daga gare ta ba.