Amsa: Suratul Asr da kuma fassarar ta:
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. {Ina rantsuwa da zamani 1. 2. Lalle ne mutum yana a cikin hasara 2. 3.Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma sukai wasiyya da gaskiya kuma sukai wasiyya da yin haƙuri 3. [Suratul Asr: 1 - 3].
FASSARA:
1. {Ina rantsuwa da zamani 1} Allah - tsarki ya tabbatar masa - ya yi rantsuwa da zamani.
2. (Lalle ne mutum yana a cikin hasara 2}: Wato: Dukkanin mutum yana cikin tawaya da kuma halaka.
3. {Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma sukai wasiyya da gaskiya kuma sukai wasiyya da yin haƙuri 3}: Sai dai wanda ya yi imani kuma ya yi aiki na ƙwarai, tare da haka suka yi kira zuwa ga gaskiya, kuma suka yi haƙuri akansa, to waɗannan sune waɗanda suka tsira daga hasara.