Amsa: Suratut Takatur da fassarar ta:
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. {Alfahari da yawan dukiya da dangi ya shagaltar da ku 1. .2. Har kuka ziyarci maƙabartu 2. 3. A'aha! (Nan gaba) zã ku sani 3. 4.A'aha! dai (Nan gaba) zã ku sani 4. 5. Haƙĩƙa, da kuna da sani sani na yaƙĩni 5. 6.Lalle ne zakuga Jahim 6. 7. Sannan kuma lalle ne za ku ganta da idanu, bayyane 7. 8. Sannan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni'imar (da aka yi muku) 8. [Surat At-Takasur: 1 - 8].
FASSARA:
1. {Alfahari da yawan dukiya da dangi ya shagaltar da ku 1}: Alfahari da dukiya da kuma 'ya'ya sun shagaltar da ku - yaku mutane - daga bin Allah.
.2. {Har kuka ziyarci maƙabartu 2}: Har kuka mutu kuka shiga ƙaburburan ku.
3. {A'aha! (Nan gaba) zã ku sani 3}: Abinda yakasance tare da ku har alfahari ya shagaltar da ku daga ƙin bin Allah, to da sannu za ku san ƙarshen wannan shagaltarwar.
4. {A'aha! dai (Nan gaba) zã ku sani 4}: Sannan za ku san ƙarshensa.
5. {Haƙĩƙa, da kuna da sani sani na yaƙĩni}:Tabbas da a ce ku kuna sani na haƙiƙanin cewa lalle ku za'a tasheku a gaban Allah, kuma zai saka muku akan ayyukan ku, da ba ku shagaltu da alfahari da dukiya da kuma 'ya'yaba.
6. {Lalle ne zaku ga Jahim 6}: Kuma wallahi sai kunga wuta a ranar Al-ƙiyama.
7. {Sannan kuma lalle ne za ku ganta da idanu, bayyane 7}:Sannan tabbas zaku ganta gani na haƙiƙa da babu kokwanto acikin sa.
8. (Sannan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni'imar (da aka yi muku) 8}: Sannan kuma tabbas sai Allah ya tambaye ku a kan hakan a ranar akan abin da yayi muku na ni'ima kamar lafiya da wadata da wasunsu.