Amsa: Suratul Adiyat da kuma fassararta:
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. {Ina rantsuwa da dawakai masu gudu suna fitar da kukan ciki 1. 2. Masu ƙyasta wuta ƙyastawa 2. 3. Sannan masu kai hari a loakcin Asuba 3. 4.Sai su motsar da ƙũra game da shi 4. 5. Sai su shiga, game da ita (ƙurar) a tsaknin jama'ar maƙiya 5. 6. Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijin sa 6. 7. Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifin sa akan haka 7. 8. Kuma lallai ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne 8. 9. Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin ƙaburbura 9. 10.Aka bayyana abin da ke cikin zukata 10. 11. Lalle ne Ubangijin su, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne? [Surat Al-Adiyat: 1 - 11].
FASSARA:
1. {Ina rantsuwa da dawakai masu gudu suna fitar da kukan ciki 1}: Allah Ya rantse da dawakai masu gudu har ake jin kukan cikin su saboda matsanancin gudu.
2. {Masu ƙyasta wuta ƙyastawa}: Kuma Allah ya rantse da dawakai waɗanda suke ƙyastawa da kofatansu idan suka taka duwatsu, saboda tsananin takawar akan su.
3. {Masu kai hari da Asuba 3}: Kuma Allah ya rantse da dawakai waɗanda suke kai hari ga abokan gaba a lokacin Asuba.
4. {Sai su motsar da ƙura game da shi 4}: Sai su motsar da ƙura saboda gudun su.
5. {Sai su shiga, game da ita a tsakanin jama'a maƙiya 5}: Sai su shiga tsakiya da sadaukan su gaba ɗaya daga maƙiya.
6. {Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa 6}: Lallai mutum mai hanawane ga alherin da Ubangijin sa Ya ke nufin sa daga gare su.
7. {Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifin sa da haka 7}: Lallai cewa shi mai shaida ne akan hanawar sa ga alheri. kuma ba zai taɓa musun haka ba saboda bayyanar sa.
8.{Kuma lalle ne shi ga dukiya shi mai tsananin so ne 8}: Lallai cewa shi saboda tsananin son sa ga dukiya yana rowa da ita ne.
9. {Shin, ba ya sanin cewa idan aka tone abin da yake cikin ƙaburbura 9}: Shin yanzu wannan mutumin mai ruɗuwa da rayuwar duniya idan Allah Ya tayar da waɗanda ke cikin ƙabarbura na matattu, kuma ya fito da su zuwa doran ƙasa domin hisabi da sakamako, to lalle al'amarin bai kasance kamar yanda yake tsammani ba?!
10. {Aka bayyana abinda ke cikin zukata 10}: Kuma aka futo, aka bayyanar da abinda yake cikin zukata na niyyoyi, da ƙudurce-ƙudirce da wasun su.
11. {Lalle ne Ubanginsu game da su a ranar nan, mai ƙididdiga ne 11}: Wato lalle Ubangijinsu dangane da su a wannan ranar wanda zai ba su labari ne, babu wani abinda yake ɓoyuwa a gare shi na al'amarin bayin sa, kuma zai yi musu sakayya akan hakan.