Tambaya ta: 2. Ka karanta Suratul Zalzala. kuma ka fassara ta.

Amsa: Suratul Zalzala da kuma Tafsirinta:

Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.

{Idan aka girgiza ƙasa, girgizawarta 1. Kuma ƙasa ta fitar da kayanta, masu nauyi 2. Kuma mutum ya ce "Mẽ neya same ta 3?. A rãnar nan, zã ta faɗi lãbãrinta 4. Da cewa Ubangijinka Ya yi umurni zuwa gare ta 5. A rãnar nan mutane zasu fito dabam-dabam domin a nuna musu ayyukansu 6. To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai gan shi 7. Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi 8. [Surat Al-Zilzilah; 1 - 8].

FASSARA:

1- {Idan aka girgiza ƙasa girgizawar nan tata}. Idan aka motsa ƙasa motsawa mai tsanani wanda zai faru gare ta a ranar Al-ƙiyama.

2- {Kuma ƙasa ta fitar da naunye nauyen nan na ta 2}: Kasa ta fitar da duk abinda yake cikinta na matattu da waninsu.

3. {Kuma mutum ya ce me ya sa me ta 3}. Mutum yana mai ɗimaucewa sai ya ce: Wanne al'amari ƙasa take ciki tana motsawa kuma tana bugawa?

4. A wannan ranar za ta ba da labarinta 4}: Acikin wannan yinin mai girman ƙasa za ta bada labari da abinda aka aikata akanta na alkhairi ko na sharri.

5. {Saboda Ubangikinka ya yi mata wahayi 5}: Domin cewa Allah Ya sanar da ita kuma Ya umarce ta da hakan.

6. {Awannan ranar mutane za su fito daban daban domin a nuna musu ayyukansu 6}. A wannan yini mai girman ne wanda ƙasa take girgiza acikinsa, mutane za su fito daga matsayar hisabi a rarrabe؛ domin su ga ayyukan su da suka aikata su a nan duniya.

7. {Wanda ya aikata nauyin komayya na alheri zai gan shi 7}: Wanda ya aikata nauyin ƙaramar tururuwa na ayyukan alheri da biyayya zai gan shi a gabansa.

8. {Wanda ya aikata nauyin komayyana na sharri zai gan shi 8}: Haka kuma duk wanda ya aikata nauyinta na ayyukan sharri zai gan shi a gaban sa.