Amsa: Suratul Nas da fassarar ta:
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
{Ka ce: "ina neman tsari ga Ubangijin mutane 1}. Mamallakin mutane 2. Ubangijin Mutane 3. Daga sharrin mai sanya wasuwãsi, mai ɓoyewa 4. Wanda ke sanya wasuwãsi a cikin ƙirãzan mutane 5. Daga Aljannu da mutane 6}. [Suratun Nas: 1 - 6].
FASSARA:
1. {Ka ce "ina neman tsari ga Ubangijin mutane 1}: Ka ce - Ya kai wannan manzo -: Ina neman kariya da Ubangijin mutane, kuma ina neman kulawar sa.
2. {Mamallakin mutane 2}: Wanda Yake tasarriufi acikin su da abin da ya ga dama, ba su da wani mamallaki in ba shi ba.
3. {Ubangijin Mutane 3}: Abin bautar su da gaskiya, babu wani abin bauta gare su da gaskiya in ba shi ba.
4. {Daga sharrin mai sanya wasawasi, mai boyewa 4}: Daga sharrin shaiɗan wanda yake jefa waswasin sa ga mutane.
5. {Wanda yake sanya wasuwãsi a cikin ƙirãzan mutane 5}: Yake jefa wasiwasin sa a zukatan muta ne.
6. {Daga Aljannu da mutane 6}: Wato: Mai jefa wasawasin yana kasancewa daga cikin mutane kuma yana kasancewa daga cikin Aljannu.