Suratut Falak da kuma fassarar ta:
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. {Ka ce "ina neman tsari ga Ubangijin safiya 1. Daga sharrin abin da Ya halitta 2. Daga sharrin dare, idan ya yi duhu 3. Daga sharrin mãtã mãsu tõfi a cikin kuduri 4. Daga sharrin mai hasada idan ya yi hasada 5}. [Surat Al-falaƙ: 1 - 5].
FASSARA:
1. {Ka ce "ina neman tsari ga Ubangijin safiya 1}: Ka ce - Ya kai wannan manzo -: Ina neman kariya daga Ubangijin safiya, ina kuma neman tsarin sa.
2. {Daga sharrin abin da Ya halitta 2}: Daga sharrin abin da zai cuitar daga halittu.
3. {Da sharrin dare, idan ya yi duhu 3}: Ina neman kariya daga Allah daga sharrikan abin da yake bayyana cikin dare na dabbobi da 'yan fashi.
4. {Daga sharrin mãtã mãsu tõfi a cikin kuduri 4}: Ina neman kariya daga gare shi daga sharrin matsafa waɗanda suke tofi a guduri (ƙulli).
5. {Daga sharrin mai hasada idan ya yi hasada 5}: Daga kuma sharrin mai hasada mai ƙiyayya ga mutane, idan yayi musu hassada akan abin da Allah ya ba su na ni'imomin sa, yana son gushewar su daga gare su, da kuma afka cuta da su.