Tambaya ta 15. Ka karanta Suratul Ikhlas kuma ka fassara ta.

Amsa: Suratul Ikhlas da fassarar ta:

Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.

1. {Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci 1. Allah shi ne abun nufi da bukata 2. 3 Bai haifa ba kuma ba'a haife shi ba 3. 4. Kuma babu ɗaya da ya kasance kini a gare Shi 4}. [Surat Al-Ikhlas: 1 - 4].

FASSARA:

1. {Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci 1} Ka ce: - Ya kai wannan manzo: - Shi ne Allah wanda babu abin bautawa da gaskiya sai shi.

2. {Allah shi ne abun nufi da buƙata 2} Wato: Shi ne wanda ake ɗaga bukatun halittu zuwa gare shi.

3 {Bai haifa ba kuma ba'a haife shi ba 3}: Ba shi da ɗa, tsarki ya tabbata a gare shi, kuma ba shi da uba.

4. {Kuma babu ɗaya da ya kasance kini a gare Shi 4}: Babu kwatankwacin sa a halittar sa.