Tabaya ta 11: Karanta Suratul Masad, kuma ka fassara ta.

Amsa: Suratul Masad da kuma Tafsirin ta:

Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.

1. {Hannãye biyu na Abũlahabi sun taɓe, kuma ya taɓe 1. 2. Dũkiyarsa ba ta tsare masa kõme ba, da abin da ya tãra 2. 3. Zãi shiga wuta mai hũruwa 3. 4. Da kuma matarsa mai ɗaukar iatacen (wuta) 4. 5. A cikin kyakkyãwan wuyanta akwai igiya ta kaba (Rãnar ¡iyãma) 5}. [Surat Al-Masad: 1 - 5].

FASSARA:

1. {Hannãye biyu na Abũlahabi sun taɓe, kuma ya taɓe 1}: Hannayan Abu Lahab sun yi asara, wanda yake kuma shi ne baffan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - Abu lahab ɗan Abdul muɗallabi, saboda taɓewar aikin sa, domin ya kasance yana cutar da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -, kuma aikin sa ya taɓe.

2. {Dũkiyarsa ba ta tsare masa kõme ba, da abin da ya tãra 2}: Wane abu ne dukiyar sa da 'ya'yan sa suka tsinana masa? ba su kare shi daga azaba ba, kuma ba su jawo masa rahama ba.

3. {Zãi shiga wuta mai hũruwa}: Zai shiga wata wuta mai huruwa ranar Al-ƙiyama da zai yi fama da zafin ta.

4. {Da kuma matarsa mai ɗaukar iatacen (wuta): Kuma da sannu matar sa Ummu Jamil wacce ta kasance ita ma tana cutar da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ta hanyar zuba ƙaya akan hanyar sa, zata shiga wutar.

5. {A cikin kyakkyãwan wuyanta akwai igiya ta kaba (Rãnar ƙiyãma) 5}: A wuyan ta igiya ce mai ingancin tufkewa za'a koro ta da ita zuwa wuta.