Tambaya ta: 13. Ka ranta Suratul Nasr? kuma ka fassara ta.

Amsa Suratul Nasr da kuma fassarar ta:

Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.

1. {Idan taimakon Allah ya zo da buɗi 1. 2. Kuma ka ga mutane suna shiga addinin Allah, jama'a jama'a 2. 3. To, ka yi Tasbihi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka nẽme Shi gafara, lalle Shi (Ubangijinka) Ya kasance Mai karɓar tũba ne 3}. [Surat Al-Nasr; 1 - 3].

FASSARA:

1. {Idan taimakon Allah ya zo da cin nasara 1} Idan taimakon Allah ya zo wa addinin ka - ya kai wannan manzo - da kuma yadda ya ƙarfafi addinin, kuma buɗe Makkah ya faru.

2. {Kuma ka ga mutane suna shiga addinin Allah, jama'a jama'a 2}: Kuma ka ga mutane suna shiga addinin musulunci ƙungiya bayan ƙungiya.

3. {To, ka yi Tasbihi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka nẽme Shi gafara, lalle Shi (Ubangijinka) Ya kasance Mai karɓar tũba ne 3}: Ka sani hakan wata alama ce ta kusancin ƙarewar aikin da aka aiko ka da shi, to sai ka yi Tasbihi haɗi da godewa Ubangijinka, domin gode masa a kan wannan ni'ima ta nasara da kuma buɗe Makkah, kuma ka nemi gafarar sa, lalle shi ya kasance mai yawan karɓar tuba ne yana karɓar tuban bayinsa, kuma yana gafarta musu.