Amsa: Suratul Kafirun da fassararta:
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. {Ka ce: "Ya kũ kãfirai 1. "Bã zan bautã wa abin da kuke bautã wa ba 2 Kuma kũ, ba ku zama masu bauta wa abin da nake bautã wa ba 3. Kuma nĩ ban zama mai bautã wa abin da kuka bautã wa ba 4. {Kuma kũ, ba ku zama masu bauta wa abin da nake bautã wa ba 5. Addininku na garẽ ku, kuma addinina yanã gare ni 6}. [Surat Al-Kafirun: 1 - 6].
FASSARA:
1. Ka ce: {Ya kũ kãfirai 1} Ka ce -Ya kai wannan Manzo -Ya ku waɗanda suka kafirce wa Allah.
2. {Bã zan bautã wa abin da kuke bautã wa ba 2}: Ba zan taɓa bautawa duka abinda kuke bautawa ba na gumaka, a yanzu ko a nan gaba.
3. {Kuma kũ, ba ku zama masu bauta wa abin da nake bautã wa ba 3}: Haka kuma ba za ku zamo masu bauta wa abin da ni na ke bautawa ba, wanda yake shi ne Allah shi kaɗai.
4. {Kuma nĩ ban zama mai bautã wa abin da kuka bautã wa ba 4}: Ni kuma ba zan bautawa abinda kuka bauta wa na gumaka ba.
5. {Kuma kũ, ba ku zama masu bauta wa abin da nake bautã wa ba 5}: Haka kuma ba za ku zamo masu bauta wa abin da ni nake bautawa ba, wanda yake shi ne Allah shi kaɗai.
6.{Addininku na garẽ ku, kuma addinina yanã gare ni 6}: Addinin ku da kuka ƙirƙira yana gareku, ni kuma addini na wanda Allah ya saukar da shi agare ni yana gare ni.