Amsa: Suratul Kausar da kuma fassarar ta:
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
{Lalle ne Mu, Mun baka alheri mai yawa 1. 2. Saboda haka, ka yi salla dõmin Ubangijinka, kuma ka sõke (baiko, wato sukar raƙumi) 2. 3. Lalle mai aibanta ka shi ne mai yankakkiyar albarka 3}. [Surat Al-kausar: 1 - 3].
FASSARA:
1. {Lallai ne mu munbaka alheri mai yawa 1}: Lallai mu munzo maka - ya kai wannan Manzo - da alheri mai yawa, daga cikinsa akwai ƙoramar Al-kausara acikin Aljanna.
2. {Saboda haka, ka yi salla dõmin Ubangijinka, kuma ka sõke (baiko, wato sukar raƙumi) 2}: Sai ka bada godiyar Allah akan wannan ni'ima, ta hanyar yin sallah saboda shi kaɗai, kuma ka yi yanka, saɓanin abin da mushurukai suke aikata shi na neman kusanci ga gumakan su da yankan.
3. {Lalle mai aibanta ka shi ne mai yankakkiyar albarka 3}: Lalle mai ƙinka to shi ne abin yankewa daga dukkanin alheri, abin mantawa wanda in za'a ambace shi za'a ambace shi ne da mummuna.