Tabaya ta 10: Karanta Suratul Ma'un, kuma ka fassara ta.

Amsa: Suratul Ma'un da kuma fassarar ta:

Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.

1. {Shin, ka ga wanda ke ƙaryatãwa game da sakamako 1? 2. To, wannan shi ne ke tunkuɗe marãya (daga haƙƙinsa) 2. 3. "Kuma ba ya kwaɗaitarwa ga (bãyar da) abincin matalauci 3. 4. To, bone ya tabbata ga masu yin salla 4. 5. Waɗanda sune masu shagala daga sallar su 5. 6. Waɗanda sune suke yin riya (ga ayyukan su) 6. 7. Kuma suna hana taimako 7}. [Surat Al-Ma'un: 1 - 7].

FASSARA:

1. {Shin, ka ga wanda ke ƙaryatãwa game da sakamako 1?}: Shin kasan wanda yake ƙaryata sakamako a ranar Al-ƙiyama?!

2. {To, wannan shi ne ke tunkuɗe marãya (daga haƙƙinsa) 2.To shi ne wannan wanda ya ke tunkuɗe maraya da ƙarfin gaske daga barin buƙatun sa.

3. {Kuma ba ya kwaɗaitarwa ga (bãyar da) abincin matalauci 3}: Ba ya kwaɗaitar da kansa ba kuma ya kwaɗaitar da waninsa akan ciyar da mabuƙaci.

4. {To, bone ya tabbata ga masu yin sallah 4}: Hallaka da azaba sun tabbata aga masu sallah.

5. {Waɗanda suke masu shagala daga sallarsu 5}: Waɗanda sune dangane da sallar su suna wasa da ita ba sa damuwa da ita har lokacinta ya fita.

6. {Waɗanda suke yin riya (ga ayyukansu) 6}: Wato su ne waɗanda suke nuna sallar su da ayyukansu, ba sa yin aiki domin Allah.

7. {Kuma suna hana taimako 7}: Suna hana taimakon wasu a abin da babu wata cutarwa a taimakon da shi.