Amsa: Suratul Fatiha da kuma Tafsirinta.
{Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai 1. Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai 2. Mai Rahama Mai Jin ƙai 3. Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako 4. Kai kaɗai muke bautawa, kuma Ka kaɗai muke neman taimakonKa 5. Ka shiryar da mu hanya madaidaiciya 6. Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi akan su ba, kuma ba ɓatattu ba 7}. [Fatiha: 1-7].
FASSARA:
An ambaceta Suratul Fatiha ne؛ domin buɗe littafin Allah da ita.
1- {Da sunan Allah mai yawan rahama ma yawan jinƙai 1.} Ma'ana: Da sunan Allah nake fara karatun Al-ƙur'ani, ina mai neman taimako da shi - maɗaukakin sarki - ina mai neman albarka da ambaton sunan sa.
{Allah}. Wato: Abin bautawa da gaskiya, kuma ba'a ambaton wanin sa da shi - tsarki ya tabbatar masa.
{Ar-Rahman}. Wato: Ma'abocin yalwatacciyar rahama, wacce rahamar sa ta yalwaci dukkan komai.
Arrahim.Mai keɓantacciyar rahama ga muminai kaɗai.
2- {Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai}. Wato: Dukkanin nau'ukan yabo da cika sun tabbata ga Allah shi kaɗai.
3. {Mai yawan rahama mai yawan jin ƙai}. Wato: Mai yalwatacciyar rahama, wacce ta yalwaci kowanne abu, kuma ma'abocin rahama mai saduwa ga muminai.
4. {Mamallakin ranar sakamako}. Itace ranar Al-ƙiyama.
5. {Kai kaɗai muke bautawa kuma gareka kaɗai muke neman taimako}. Wato: Muna bauta maka kai kaɗai kuma muna neman taimako da kai kai kaɗai.
6. {Ka shiryar da mu hanya madaidaiciya}. Itace shiriya zuwa Musulunci da kuma Sunnah.
7. {Hanyar waɗanda ka yi ni'ima agaresu , ba waɗanda ka yi fushi da su ba, ba kuma ɓatattu ba 7}. Wato: Tafarkin bayin Allah na gari daga Annabawa da waɗanda suka biyo su, ba hanyar Nasara da Yahudu ba.
-An sunnanta bayan karanta ta yace (AMIN) wato: Ka amsa mana.