Amsa: Ka wanke tafuka sau uku.
Sai kayi kuskurar baki ka shaƙa ruwa, ka kuma face sau uku.
Kuskurar baki: Shine sanya ruwa a baki, da kuma karkaɗa shi, da zubar dashi.
Shaƙa ruwa: Shine: Jan ruwa ne ta iska zuwa cikin hanci da hannun damansa.
Facewa: Shine fitar da ruwa daga hanci bayan shaƙawa, da hannun hagunsa.
Sannan wanke fuska sau uku.
Sannan wanke hannuwa biyu zuwa gwiwar hannu sau uku.
Sannan shafar kai, zaka fuskanto da hannayenka sannan kayi baya, sai ka shafi kunnuwa biyu.
Sannan ka wanke ƙafafuwanka biyu zuwa idan sawu sau uku.
Wannan shine mafi cika, haƙiƙa wannan ya tabbata daga Annabi - tsira da amincin Alla su tabbata agareshi - acikn hadisai acikin Bukhari da Muslim, waɗanda Usman da Abdullahi ɗan Zaid da wasunsu suka ruwaitosu. Kuma haƙiƙa ya tabbata a Bukhari da waninsa: "Lallai cewa shi yayi alwala sau ɗai-ɗai, kuma cewa shi yayi alwala sau biyu-biyu", ma'ana: Lallai cewa shi yana wanke kowacce gaɓa daga gaɓɓan alwala sau ɗai-ɗai, ko sau biyu-biyu.