Tambaya ta 37. Kayi bayanin Azimi?

Amsa- Shine yin bauta sabo da Allh ta hanyar kamewa daga barin abinda ke karya azumi, tun daga hudowar Alfiji har zuwa faɗuwar rana tare da niyya, shi kashi biyune:

Azumin wajibi: Kamar Azumin watan Ramadan, shi kuma rukuni ne daga cikin rukunan musulunci.

Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan waɗanda suke daga gabãninku, tsammãninku, zã ku yi taƙawa}. [Surat Al-Baƙarah: 183].

Da Azumin da bana wajibi ba: Kamar Azumin ranar Litinin da Alhamis a kwanne sati, da Azumin kwanaki uku a kowanne wata, mafificin su kuma sune fararan kwanaki (13,14,15) na kowanne watan Musulunci.