Tambaya ta: 3. Menene falalar Alwala?

Amsa- Annabi - tsira da aminci su tabbata agareshi - yace: "Idan bawa musulmi yayi alwala", ko kuma "Mumini", "sai ya wanke fuskarsa, to kowane kuskure zai fita daga fuskarsa da yayi duba zuwa gareshi da idanuwansa tare da ruwan", ko kuma "Tare da ƙarshen ɗigon ruwan", "Idan ya wanke hannayensa, kowane kuskure zai fita daga hannayensa waɗanda hannayensa suka damƙa dasu tare da ruwan" ko "Tare da ƙarshen ɗigon ruwan", "Idan ya wanke kafafuwansa kowane kuskuren da ƙafafuwansa suka tafi garesu zasu fita tare da ruwa ko tare da ƙarshen ɗigon ruwan" "Har sai ya fita tsarkakakke daga zunubai". Muslim ne ya rawaitoshi.