Tambaya ta: 28.Wacce rana ce mafi falala a mako?

Amsa: Ranar Juma'a, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - yace: "Lalle yana daga cikin mafificin ranakunku ranar Juma'a, acikintane aka halicci Annabi Adam, kuma acikintane aka karɓi rayuwarsa, kuma acikintane za'a busa ƙaho, kuma acikintane za'a mutu, ku yawaita yin salati agareni acikinta, domin salatinku abin bijirowane agareni". Yace: Sukace Ya Ma'aikin Allah, to yaya za a bijiro da salatimmu agareka alhali haƙiƙa ka dandaƙe? - suna cewa ka dandaƙe - sai yace: "Lalle Allah - mai girma da ɗaukaka - ya haramta wa ƙasa jikin Annbawa". Abu Daud da waninsane suka ruwaitoshi.