Tambata ta: 25. Yaya musulmi zaiyi sallah?

Amsa: Siffar yadda ake sallah.

1.Ya fuskanci Al-ƙibla da dukkanin jiknsa, batare da karkacewaba, ko kuma waiwaye.

2. Sannan yayi niyyar sallar da yake son ya sallaceta a zuciyarsa ba tare da furta niyyar ba.

3. Sannan yayi kabbarar Harama, sai yace: (Allahu Akbar), ya ɗaga hannayensa biyu zuwa daidai da kafaɗunsa biyu yayin kabbarar.

4. Sannan yaɗora tafin hannunsa na dama a bayan tafin hannunsa na hagu a saman ƙijinsa.

5. Sannan yayi addu'ar buɗe sallah, sai yace: "Ya Allah ka nesantar da tsakanina da kurakuraina kamar yadda ka nesanta tsakanin mahudar rana da mafaɗarta, ya Allah ka tsaftaceni daga kurakuraina kamar yadda ake tsaftace farin tufa daga datti, ya Allah ka wankeni daga kurakuraina da ruwa da ƙanƙara da kuma kumfa".

“Subhanakal Lahumma Wabi Hamdika, Tabarakas Muka, Wata’ala Jadduka, Wala’ilaha Gairaka”.

6.Sannan ya nemi tsari, sai yace: "Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗan abin jefewa. 7. Sannan yayi Bisimillah, ya karanta Fatiha sai yace: {Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai 1. Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai 2. Mai Rahama Mai Jin Qai 3. Mamallakin Rãnar Sakamako 4. Kai kaɗai muke bautawa, kuma Ka kaɗai muke neman taimakonKa. Ka shiryar da mu hanya madaidaiciya 6. Hanyar waɗanda Kayiwa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi akansuba, kuma ba ɓatattu ba 7}. [Fatiha: 1-7].

Sannan yace: (Amin), yana nufin: Ya Allah ka amsa.

8.Sannan ya karanta abinda ya sawwaƙa na Al-ƙur'ani, sai ya tsawaita karatu a sallar Asuba.

9. Sannan yayi ruku'u: Wato ya sunkuyar da kansa, domin girmamawa ga Allah, ya kuma yi kabbara yayin ruku'insa, sai ya ɗaga hannayensa zuwa daura da kafaɗunsa. Sunnah: Itace ya miƙar da gadon bayansa, ya ɗora kansa daidai dashi, ya ɗora hannayensa akan gwiwowinsa biyu, yana mai wara yatsu.

10. Yana mai cewa acikin ruku'insa: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijina Mai girma}. sau uku, idan kuma ya ƙara da: "Tsarki ya tabbatar maka ya Allah da godiyarka, ya Allah ka gafartamini" to yana da kyau.

11. Sannan ya ɗago kansa daga ruku yana mai cewa: "Allah yaji wanda ya gode masa", sai ya ɗaga hannayensa a wannan lokacin zuwa daura da kafaɗunsa biyu. Mamu kuwa ba zaice: "Allah yaji wanda ya gode masa", kawai a maimakonta sai yace: "Ya Ubangijinmu godiya ta tabbata gareka".

12. Sannan yace bayan ɗagowarsa: "Ya Ubangijimmu, godiya ta tabbata gareka cikin sammai da ƙasa, da kuma cikin abinda kaso na kowanne abu bayan haka".

13. Sannan yayi sujjadar farko, sai yace ayayin sujjadarsa: "Allahu Akbar", kuma zaiyi sujjadar ne akan gaɓɓai bakwai: Goshi, da hanci, da tafukan hannu biyu, da gwiwowi biyu, da gefunan yatsun ƙafafuwa biyu, sai nisantar da damutsansa daga gefunan jikinsa biyu, kada ya shinfiɗa zangalalin hannayensa biyu akan ƙasa, ya kuma fuskanci Al-ƙibla da kan yatsunsa.

14. Sai yace acikin ruku'insa: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijina mafi ɗaukaka" sau uku, idan ya ƙara: "Tsarki ya tabbatar maka ya Allah Ubangijinmu, ya Allah ka gafarta mini" to yana da kyau.

15. Sannan ya ɗago kansa daga sujjada yana mai cewa: "Allah ne mafi girma".

16. Sannan ya zauna tsakanin sujjada biyu, akan diddigensa na hagu, sai ya kafa diddigensa na dama, sai ya ɗora hannunsa na dama akan gefan cinyarsa ta dama, daga inda yake biye da gwiwarsa, sai ya dunƙule ƙaramin yatsa da wanda yake bi masa, sai kuma ya ɗaga manuniya yana mai motsashi a yayin addu'arsa, yana sanya gefan babban yatsa haɗe da yatsan tsakiya kamar kewaye, sai ya ɗora hannunsa na hagu yatsun a shimfiɗe akan gefen cinyarsa ta hagu daga inda yake biye da gwiwa.

17. Sai yace acikin zamasa tsakanin sujjadu biyu: "Ya Ubangijina ka gafarta mini, ka ji ƙaina, ka shiryar dani, ka azurtani, ka datar dani, ka yi mini afuwa".

18. Sannan ya sake yin sujjada ta biyu kamar ta farko cikin abinda ake faɗa, kuma ake aikatawa, ya kuma yi kabbara yayin sujjadarsa.

19. Sannan ya miƙe daga sujjada ta biyun yana mai cewa: "Allah ne mafi girma" yana sallatar raka'a ta biyu kamar ta farko acikin abinda ake faɗa da abinda ake aikatawa, sai dai cewa shi ba zai sake addu'ar buɗe sallah acikinta ba.

20. Sannan ya zauna bayan ƙare raka'a ta biyu yana mai cewa: "Allah ne mafi girma", sai ya zauna kamar yadda ya zauna a tsakanin sujjada biyu daidai wadaida.

21. Sai ya karanta Tahiya a wannan zaman, sai yace: "Gaisuwa ta tabbata ga Allah da addu'oi da kyawawan abubuwa, aminci ya tabbata a gareka, ya kai wannan Annabi, da rahamar Allah da albarkarsa, aminci ya tabbata agaremu da salihan bayin Allah, ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaidawa cewa lallai Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa ne, Allah kayi tsira ga Muhammad da iyalan Muhammad, kamar yadda kayi salati ga Ibrahim da iyalan Ibrahim, lallai kai abin yabone mai girma, kayi albarka ga Muhammad da iyalan Muhammad, kamar yadda kayi albarka ga Ibrahim da iyalan Ibrahim, lallai cewa kai abin yabone kuma mai girma". Sannan sai ya roƙi Ubangijinsa da abinda yaso, na alhairan Duniya da lahira.

22. Sannan yayi sallama a damansa yana mai cewa: "Aminci ya tabbata agareku da rahamar Allah". Da kuma hagunsa kamar haka.

23. Idan sallar ta zama mai raka'a uku ce ko huɗu,ya tsaya inda ƙarshen Tahiyar farko take, shine: "Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaidawa lalle Annabi Muhammadu bawansane kuma Manzonsane".

24. Sannan sai ya yunƙura yana mai cewa: "Allah ne mafi girma", yana ɗaga hannayensa zuwa daidai kafaɗunsa a daidai wannan lokacin.

25. Sannan sai ya sallaci abinda yayi saura na sallarsa akan siffar raka'a ta biyu, sai dai cewa shi zai taƙaita ne akan karatun Fatiha kaɗai.

26. Sannan sai ya zauna zama na Tawarruƙ, yana kafa diddigen ƙafarsa tadama, yana kuma fitar da diddigen ƙafarsa ta hagu ta ƙarkashin ƙwaurinsa na dama, sai ya tabbatar da mazauninsa a ƙasa, sai kuma ya ɗora hannuwansa akan cinyoyinsa akan siffar ɗorasu aTahiyar farko.

27. A wannan zaman zai karanta Tahiya ne baki ɗayanta.

28. Sannan yayi sallama a damarsa yana cewa: "Assalamu alaikum warahmatullah". hakama a hagunsa.