Amsa- Goma shaɗaya ne, kamar yanda yake tafe:
1.Faɗinsa bayan kabbarar Harama: "Subhanakallahumma, wabi hamdika, watabarakasmuka, wa ta'ala jadduka, wa la ilaha ghairuka". Ana ambatanta: Addu'ar buɗe sallah.
2. Neman tsari.
3. Yin Bisimillah.
4. Faɗin: Amin.
5.Karatun surah bayan fatiha.
6. Bayyanar da karatu ga liman.
7.Faɗin: "Mil'us samawati, wamil'ul ardhi, wa mil'u ma shi'ita min shai'in ba'adu". Bayan kammala Tahamidi.
8. Abinda yaƙaru akan ɗaya na Tasbihin ruku'i, wato: Tasbihi na biyu da na uku da abinda ya ƙaru akan haka.
9. Abinda ya ƙaru akan ɗaya a tasbihin sujjada.
10. Abinda ya ƙaru akan ɗaya a faɗinsa: "Rabbig firli" Tsakanin sujjada biyu.
11.Yin salati a tahiyar ƙarshe ga iyalansa - tsiran da amici ya tabbata agaresu -, da albarka a gareshi da kuma su, da yin addu'a bayansa.
Na huɗu: Sunnoni na ayyuka, ana ambatansu Al-Hai'at.
1. Daga hannu tare da kabbarar Harama.
2. Da yayin yin ruku'u.
3. Da kuma lokacin ɗagowa daga ruku'in.
4. Da sakko dasu bayan hakan.
5. Dora hannun dama akan na hagu.
6. Dubansa zuwa bigiren sujjadarsa.
7. Warawarsa tsakanin diga-digansa biyu alhali yana tsaye.
8. Damƙar gwiwowinsa da hannayensa, yana mai wara yatsun hannaye a ruku'insa, da kuma miƙar da gadon bayansa acikinsa, da sanya kansa daura dashi.
9. Tabbatar da gaɓuɓuwan sujjada a ƙasa, da kuma damƙar ƙasar ga bigiren sujjada.
10. Buɗa damatsansa ga gefunansa biyu, da kuma raba cikinsa ga cinyoyinsa, da raba cinyoyinsa ga ƙwaurikansa, da rabawarsa tsakanin gwiwowinsa, da tsayar da diga-digansa, da sanya cikin yatsunsu akan ƙasa yana mai rabawa, da sanya hannuwansa daura da kafaɗunsa a shinfide, yatsun kuma a dunƙule.
11. zaman Iftirashi a zama tsakanin sudda biyu, da a zaman Tahiya na farko, da kuma zaman Tawarruk a zama na biyu.
12. Dora hannaye akan cinyoyi suna a shinfiɗe, yatsun a dunƙule tsakanin sujjadu biyu, haka kuma a Tahiya, sai dai cewa shi anan zai damƙi daga ƙaramin ɗan yatsa na gefe dama da mai binsa, yakuma naɗe babban yatsa tare da na tsakiya, yana mai nuni da manuniyarsu yayin ambaton Allah.
13. Juyawarsa dama da hagu acikin sallamarsa.