Amsa; Su rukunai goma sha huɗu ne, kamar yanda yake zuwa:
Na farkonsu: Tsayuwa acikin farilla ga mai iko.
Kabbarar Harama, itace: "Allahu Akbar".
Karatun Fatiha.
Ruku'u, sai ya miƙar da gadon bayansa adaidaice, ya kuma sanya kansa daidai da dashi.
Dagowa daga gareshi.
Daidaituwa alhali yana a tsaye.
Sujjada, da kuma tabbatar da goshinsa, da hancinsa, da tafukan hannayensa biyu, da gwiwowinsa biyu, da yatsun gefan diga-digansa daga awurin sujjadarsa.
Dagowa daga sujjada.
Zama tsakanin sujjada biyu.
Sunna: Shine ya zauna yan mai shinfiɗa akan kafarsa ta hagu, yana kuma kafe kafarsa ta dama, yana mai fuskantar da ita zuwa Al-ƙiblah.
Nutsuwa, itace natsuwa akowane rukuni na aiki.
Tahiyar ƙarshe.
Zama domin shi.
Sallama biyu, shine yace sau biyu: "Assalamu alaikum wa rahmatullah".
Jeranta rukunai - kamar yadda muka ambata -, da zaiyi sujjada a misali kafin ruku'insa da gangan to ta ɓaci, idan kuma da rafkannuwane, to dawowa ya lazimceshi dan yayi ruku'u, sannan yayi sujjada.