Tambaya ta: 33. Kayiwa waɗannan sunayen sharhi?

Amsa: ALLAHU, Ma'anarsa Allah abin bautawa da gaskiya, shi kaɗai yake bashi da abokin tarayya.

ARRABBU: Wato Mahalicci Mamallaki Mai yawan azurtawa, Mai jujjuya al'amura, shi kaɗai yake tsarki ya tabbatar masa.

ASSAMI'U: Wanda jinsa ya yalwaci kowanne abu, kuma yana jin dukkanin muryoyi akan saɓaninsu, da karkasuwarsu.

ALBASIRU: Wanda yake ganin kowanne abu, kuma yana ganin komai ya ƙaranta ko ya girmama.

AL'ALIMU: Shine wanda iliminsa ya kewaye kowanne abu, wanda ya wuce, dana yanzu, da kuma na nan gaba.

ARRAHMAN: Wanda ramhamarsa ta yawalci dukkanin abin halitta da kuma rayayye, dukkanin bayi da sauran ababen halitta suna ƙarƙashin rahamarsa ne.

ARRAZZAKU: Wanda agareshi ne arziƙin dukkanin halittu yake, daga mutane da Aljanu da sauran dukkanin dabbobi.

ALHAYYU: Shine Rayayye wanda baya mutuwa, kuma dukkanin halitta zasu mutu.

AL'AZIMU: Wanda yake da kamala da girma dukkaninsu, a sunayansa da siffofinsa da kuma ayyukansa.