Amsa:Tsoro, shine jin tsoron Allah da kuma uƙubarsa.
Kwadayi: Shine kwaɗayin ladan Allah da gafararsa, da kuma rahamarsa.
Dalili: Faɗin Allah - maɗaukakin sarki -: {Waɗancan, waɗanda suke kiran, sunã nẽman tsãni zuwa ga Ubangijinsu. Waɗanne ne suke mafĩfĩta a kusanci? Kuma sunã kwadayin sãmun rahamarsa, kuma sunã tsõron azãbarsa. Lalla ne azãbar Ubangijinka ta kasance abar tsõro ce 57}. [Surat Al-Isra'i: 57]. Kuma Allah - Maɗaukakin sarki - yace: {Ka bawa bayina labari, lalle nine Mai yawan gafarane, kuma Mai yawan jinƙaine 49. Kuma lallai azabata itace azaba mai raɗaɗi 50}. [Surat Al-Hujrat: 49-50].