Tambaya ta: 22. Menene munafinci da nau'o'insa?

Amsa:

1- Babban Munafunci: Shine ɓoye kafirci da kuma bayyanar da imani.

Yana fitarwa daga musulunci, kuma shi yana daga kafirci mafi girma.

Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Lalle munafikai suna can ƙasan ƙasa na wuta, kuma ba zaka taɓa samar musu mataimaki ba}. [Surat Al-Nisa'i: 145].

2.Karamin munafunci:

Misalin: Karya, saɓa alkawari, da cin amana.

Wannan ba ya fitarwa daga musulunci, shi yana daga cikin zunubai, kuma maiyin shi abin bijirowane ga azaba.

Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata agareshi - yace: "Alamomin munafuki uku ne: Idan yai zance sai yayi ƙarya, idan yayi alƙawari sai ya saɓa, kuma idan aka amince masa sai yayi ha'inci". Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.