Amsa: Imani da Allah.
Ka yi imani da cewa Allah shi ne wanda ya halicceka kuma ya azurtaka, shine kuma mamallakin halittu mai jujjuya lamuran halittu shi kaɗai.
Shine kuma abin bautawa, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai shi.
Kuma shi ne mai cikakken girma, wanda yake dukkan godiya ta tabbata gareshi, kuma shi ke da sunaye kyawawa da kuma siffofi maɗaukaka, bashi da abokin tarayya, kuma wani abu baiyi kama dashi ba, tsarki ya tabbatar masa.
Imani da Mala'iku:
Sune ababen halittar da Allah ya halicce su daga harske,kuma domin bautarsa, da cikakken jawuwa ga umarninsa.
Daga cikinsu akwai Jibrilu - amincin Allah ya tabbata agareshi - wanda yake saukar da wahayi ga Annabawa.
Imani da Litattafai:
Sune littattafan da Allah ya saukar da su ga Manzanninsa.
- Kamar Al-ƙur'ani: Ga Annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -.
- Injila: Ga Annabi Isa - amincin Allah ya tabbata agareshi -.
- Attaura ga Annabi Musa - amincin Allah ya tabbata agareshi -.
- Zabura ga Annabi Dawud - amincin Allah ya tabbata agareshi -.
- Takardun Annabi Ibrahim da Annabi Musa; Ga Ibrahim da Musa.
Imani da Manzanni:
Sune waɗanda Allah ya aiko su zuwa ga bayinsa, domin su ilmantar dasu, kuma suyi musu bushara da alheri da Aljanna, su kuma yi musu gargaɗi da sharri da kuma wuta.
- Mafifitansu: Sune Ulul Azmi, sune:
Annabi Nuhu - aminci ya tabbata agareshi -.
Annabi Ibrahim - aminci ya tabbata agareshi -.
Annabi Musa - aminci ya tabbata agareshi -.
Annabi Isa - aminci ya tabbata agareshi -.
Annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -.
Imani da Ranar Lahira:
Shine abinda yake bayan mutuwa, a ƙabari, da ranar Al-ƙiyama, ranar tashi daga ƙabari, da hisabi, yadda 'yan Aljanna zasu tabbata acikin masaukansu, da 'yan wuta acikin masaukansu.
Imani da ƙaddara alherinsa da kuma sharrinsa:
Kaddara: Shine ƙudurcewa a zuciya cewa Allah yana sanin dukkan wani abu da yake kasancewa a kasantattu, kuma cewa shi ya rubuta wannan abin acikin Lauhul Mahfuz, kuma yaso samuwarsa da kuma halittarsa.
Allah - maɗaukakin sarki - yace: {Lalle ne mu kowanne abu mun halicce shi da ƙaddara 49}, [Suratu Al-kamar: 49].
- Shi yana kan matakai huɗu:
Na ɗaya: Sanin Allah - maɗaukakin sarki - yana daga wannan saninsa wanda ya rigayi dukkan komai, kafin afkuwar abubuwa da bayan afkuwarsu.
Dalilinsu: faɗin Allah - maɗaukakin sarki -: {Lalle Allah a wurinsane kawai sanin Al-ƙiyama, kuma yanã saukar da girgije, kuma yanã sanin abin da yake a cikin mahaiffannai, kuma wani rai bai san abin da zai aikatãba a gõbe, kuma wani rai bai san a wace ƙasã zai mutuba. Lalle Allah Masani ne Mai bada labari 34}. [Suratu Luƙman: 34].
Na biyu: Cewar Lallai ya rubuta wannan a Lauhul Mahfuz, dukkan wani abu da ya kasance, da kuma zai kasance to a rubuce yake a wurin Allah a cikin littafi.
Dalilinta: Faɗin Allah - maɗaukakin sarki -: {Kuma a wurinSa mabũɗan gaibi suke, babu wanda yake sanin su fãce shi, kuma yanã sanin abin da ke a cikin sarari da kogi, kuma wani ganye ba ya fãɗuwa, fãce yã san shi, kuma bãbu wata ƙwãya a cikin duffan ƙasã, kuma babu ɗanye, kuma babu ƙẽƙasasshe, fãce yanã a cikin wani Littãfi mai bayyanãwa 59}. [Suratu Al-An'am: 59].
Na Uku: Shine kowannce abu da yake faruwa da ganin damar Allah ne, babu wani abu dazai faru daga gare shi ko kuma daga halittarsa sai da ganin damarsa - maɗaukakn sarki -.
Dalilinta: Faɗin Allah - maɗaukakin sarki -: {Ga wanda yaso daga cikinku to ya tsaya kan tafarki madaidaici 28 kuma ba komai kuke nufin aikatawa ba sai in Allah ya so, shine Ubangijin talikai}. [Suratu Al-Takwir: 28,29].
Na huɗu: Imani da cewar dukkanin kasantattu ababen halittane Allah ya haliccesu, kuma ya halicci zatinansu da siffofnsu da motsinsu, da dukkanin wani abu acikinsu.
Dalilinta: Faɗin Allah - maɗaukakin sarki -: {Allah ne ya halitta ku da abin da kuke aikatãwa 96}. [Suratu Al-Saffat: 96].