Tambaya 13. Shin wani ɗaya wanda ba Allah ba ya san gaibu?
Amsa- Babu wani wanda yasan gaibu sai Allah shi kaɗai.
Allah -maɗaukakin sarki - yace:{Kace bãbu wanda ya san gaibi a cikin sammai da ƙasa fãce Allah. Kuma bã su sansancẽwar a yaushe ne zã a tãyar da su 65}. [Suratu Al-Naml: 65].