Amsa- Shirka: Itace juyar da kowane nau'i daga cikin nau'ikan ibada ga wanin Allah - maɗaukakin sarki -.
Nau'ukanta:
Babbar shirka, Misali: Kiran wanin Allah - maɗaukakin sarki -(kira na bauta) ko yin sujjada ga wanin Allah - tsarki ya tabbatar masa - ko kuma yanka ga wanin Allah - mai girma da ɗaukaka -.
Karamar Shirka, misali: Rantsuwa da wanin Allah - maɗaukakin sarki -,ko layu, shine abinda ake ratayawa daga abubuwa dan jawo wani amfani, ko tunkuɗe wata cuta, da sassauƙan riya, kamar ya kyautata sallarsa dan abinda yake gani daga kallon mutane zuwa gareshi.