BANGARAN LADUBBAN MUSULUNCI

Amsa: 1. Girmama shi - tsarki ya tabbatar masa ya ɗaukaka -.

2. Bauta masa shi kaɗai ba shi da abokin tarayya.

3. Yi ma sa biyayya.

4. Barin saɓa ma sa.

5. Gode ma sa da yaba ma sa - ya girma ya ɗaukaka - akan falalar sa da ni'imomin sa waɗanda ba za su lissafu ba.

6. Yin haƙuri akan abubuwan da ya ƙaddara.

Amsa: 1. Bin sa da kuma koyi da shi.

2. Yi masa biyayya.

3. Barin saɓa ma sa.

4. Gasgata shi a dukkanin abin da ya bada labari.

5. Rashin ƙirƙira acikin ɗari akan sunnar sa.

6. Son sa sama da rai da kuma dukkanin mutane.

7. Girmama shi da taimakon sa da kuma taimakon Sunnar sa.

Amsa: 1. Yi wa iyaye biyayya a duk abinda yake ba saɓon Allah bane.

2. Yi wa iyaye hidima.

3. Taimakawa iyaye.

4.Biyan buƙatun iyaye.

5. Yin addu'a ga iyaye.

6. Yin ladabi tare da su a magana, faɗin: "tsaki" baya halatta, shi ne kuwa mafi ƙarancin maganganu.

7. Yin murmushi a fuskar iyaye, kar ka ɗaure fuska.

8. Ba zan ɗaga murya ta ba sama da ta iyaye, zan kuma saurare su, ba kuma zan katse su ba da zance, ba kuma zan kira su da sunan su ba, sai dai zan ce: "Babana", "Babata".

9. Zan nemi izini kafinin shiga ga babana da babata alhali su suna cikin ɗaki.

10. Sumbantar hannu da kan iyaye.

Amsa: 1. Ziyartar dangi na kusa, kamar: Dan uwa, da 'yar uwa, da baffa da gwaggo da kawu da inna, da sauran 'yan uwa.

2. Kyautata mu su,ta hanyar magana da aiki da kuma taimaka mu su.

3. Yana cikin haka buga musu waya da kuma tambayar halin da suke ciki.

Amsa: 1. Ina so kuma ina abota da mutanan ƙwarai.

2. Ina nisanta kuma ina barin mutanen banza.

3. Ina yin sallama ga 'yan uwana kuma ina musafaha da su.

4. Ina zuwa gaida su idan ba su da lafiya, kuma ina musu addu'ar samun sauƙi.

5. Ina gaida wanda ya yi atishawa.

6.Ina amsa gayyatar sa idan ya gayyaceni dan ziyartar sa.

7. Ina kuma yi masa nasiha.

8. Ina taimaka ma sa idan aka zalunce shi, ina kuma hana shi yin zalunci.

10.Ina so wa ɗan'uwa na musulmi abin da nake so wa kaina.

11. Ina taimaka masa idan ya buƙaci taimako na.

12. Bazan shafe shi da cuta ba, da magana ko da aiki.

13. Ina ɓoye masa sirrin sa.

14. Ba na zagin sa, kuma ba na gulmar sa. sannan ba na wulaƙanta shi, kuma ba na yi masa hassada, kuma ba na masa binciken ƙwaƙwaf, kuma ba nayi masa maguɗi.

Amsa: 1. Ina kyautata wa maƙoci ta hanyar magana da aiki, kuma ina taimaka masa idan ya buƙaci taimako na.

2. Ina mishi barka idan yana farin ciki da idi (sallah ƙarama ko babba) ko aure ko ma wanin haka.

3. Ina gaida shi idan ya yi rashin lafiya, kuma ina taya shi alhini idan wata masifa ta afka ma sa.

4. Ina ba shi irin abin cin da nayi gwargwadon iko.

5. Ba na riskar da cuta da shi, da wata magana ko da wani aiki.

6. Ba na damun sa ta ɗaga murya, ko in yi mishi leƙen asiri, kuma ina yin haƙuri da shi.

1. Ina amsa wa duk wanda ya kira ni zuwa baƙuncin sa.

2. Idan ina son in ziyarci wani, ina neman izinin sa da kuma lokacin.

3. Zan nemi izini kafin in shiga.

4. Ba na jinkiri a ziyara.

5. Ina runtse idanu dangane da iyalan gidan.

6. Ina madalla da baƙo kuma ina tarbar shi da kyakkyawa tarba, da sakin fuska, da kyakkyawar magana ta maraba lale.

7. Ina saukar da baƙo a mafi kyawun wuri.

8. Ina kuma girmama shi ta hanyar shirya garar baƙi, na abinci da abin sha.

Amsa: 1. A lokacin da nake jin raɗaɗi, ina ɗora hannu na na dama a wurin sa, sai in ce: "Bismillah". Sau uku, sai kuma in ce: "Ina neman tsari da buwayar Allah da kuma ikoin sa (ya kare ni) daga sharrin abinda nake ji, kuma nake tsoro". Sau bakwai.

2. Ina yarda da abinda Allah ya ƙaddara shi, kuma ina haƙuri.

3. Ina gaggawar ziyartar ɗan uwa na mara lafiya, kuma ina ma sa addu'a, ba na tsawaita zama a wurin sa.

3. Ina masa addu'a ba tare da ya nema daga gareni ba.

5. Ina yi masa wasiyya da yin haƙuri da addu'a, da kuma sallah da tsarkaka gwargwadon yanda zai iya.

5.Addu'a ga maralafiya: "Ina roƙon Allah mai girma, Ubangijin Al'arshi maigirma da ya baka lafiya". Sau bakwai.

Amsa: 1. Tsarkake niyya domin Allah - mai girma da ɗaukaka -.

2. Ina aiki da ilimin da nake neman sanin sa.

3. Ina girmama malami, kuma ina mutunta shi a gaban sa da fakuwarsa.

4. Ina zama a gaban sa cikin ladabi.

5. Ina yin shiru gare shi sosai, ba na katse shi a karatun sa.

6.Ina ladabi wurin gabatar da tambaya.

7, Ba na kiran sa da sunan sa.

Amsa: 1. Zan yi sallama ga ma'abota wurin zaman.

2. Ina zama inda wurin zama ya tiƙe da ni, ba zan tayar da wani daga inda yake zaune ba, ko in zauna tsakanin mutane biyu, sai da izinin su.

3. Zan buɗa wuri domin wani na ya ya zauna.

4. Ba zan katse maganar (da ake yi) a wurin zaman ba.

5. Ina neman izini, kuma ina yin sallama kafin juyawa daga wurin zaman.

6. Alokacin da majalisar ta ƙare ina yin addu'ar da ake yi Kaffaratul Majlis. "Tsarki ya tabbatar maKa da godiyar Ka, ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, ina neman gafararKa kuma ina tuba zuwa gareKa".

Amsa: 1. Ina bacci da wuri.

2. Ina yin bacci acikin alwala.

3. Ba na bacci rub da ciki.

4. Ina kwanciya a gefa na na dama, sai in sanya hannuna na dama a ƙarƙashin kunci na na dama.

5. Ina karkaɗe shinfiɗa ta.

6.Ina karanta zikiran kwanciya bacci, kamar karanta Ayatul Kursiyy, Suratul Ikhlas, Falaƙi da Nasi. Sau uku Sai in ce: "Da sunanKa Ya Allah nake mutuwa, kuma nake rayuwa".

7. Ina tashi domin yin sallar Asuba.

8. Sai in ce bayan na farka daga bacci: "Dukkan godiya ta tabbata ga Allah wanda ya rayar da mu bayan ya matar da mu, kuma taruwa gare shi take".

Amsa:

1. Ina yin niyya a cin abin ci na da shan abin sha na samun ƙarfi akan bautar Allah - mai girma da ɗaukaka -.

2. Wanke hannuwa biyu kafin cin abin ci.

3. Ina cewa: "Da sunan Allah", ina kuma ci ne da hannu na na dama, kuma (ina cin) abinda ke gaba na, ba na ci daga tsakiyar akussa, ko kuma daga gaban wani na.

4. Idan na manta ambaton Allah, sai in ce: "Da sunan Allah a farkon sa da ƙarshen sa".

5. Ina yarda da abinda aka samu na abinci, ba kuma na aibata abinci, idan ya ƙayatar da ni sai in ci shi, idan kuma bai ƙayatar da ni ba sai in bar shi.

6. Ina ci laumoni ne kaɗan, ba na ci da yawa.

7. Ba na busa acikin abin ci ko abin sha, ina barinsa ne har ya huce.

8. Ina taruwa ne da wani na a abin ci, tare da iyali ko baƙo.

9. Ba na fara cin abin ci kafin wani na daga wanda shine mafi girma gare ni.

10. Ina ambaton Allah alokcin da zan sha, kuma ina sha ne a zaune, kuma a kwankwaɗa uku.

11. Ina godewa Allah yayin da na gama daga abincin.

Amsa: 1. Ina fara sanya tufafi na ne ta dama, kuma ina godewa Allah akan hakan.

2. Ba na sakin tufafi har yakai ƙasan idon sawu.

3. 'Ya'ya maza ba sa sanya tufafin 'ya'ya mata, haka kuma 'ya'ya mata ba sa sanya tufafin 'ya'ya maza.

4. Rashin yin kamanceceniya da tufafin kafirai ko fasiƙai.

5.Yin Bisimillah lokacin cire tufafi.

6. Sanya takalmi da (ƙafar) dama a farko, da kuma cirewa da (ƙafar) hagu.

Amsa: 1. Ina faɗin: "Da sunan Allah, kuma godiya ta tabbata ga Allah". {Tsarki ya tabbata ga wanda ya hore mana wannan, alhali kuwa ba mu kasance masu iya rinjaya gare shi ba 13. Kuma lalle mũ haƙĩƙa mãsu jũyãwa muke, zuwa ga Ubangijinmu 14}. [Surat Al- Zukhruf 13-14].

2. Idan na wuce musulmi sai in yi masa sallama.

Amsa: 1.Ina daidaituwa kuma ina ƙanƙar da kai a tafiya ta, ina kuma tafiya ne ta daman hanya.

2. Ina yin sallama ga duk wanda na haɗu da shi.

3. Ina rintse idanu na, ba kuma na cutar da kowane ɗaya.

4. Ina yin umarni da kyakkyawan aiki, ina kuma hani daga mummuna.

5. Ina gusar da ƙazanta daga hanya.

Amsa: 1. Ina fita ne da ƙafa ta ta hagu, sai in ce: "Da sunan Allah, na dogara ga Allah, babu ƙarfi babu dabara sai ga Allah, Ya Allah lallai ni ina neman tsarin Ka akan kada in ɓata ko aɓatar da ni, ko in karkace ko a karkatar da ni, ko in yi zalinci ko a zalince ni, ko in yi wawanci ko a yi wawanci akaina". 2. Ina shiga gida da ƙafa ta ta dama, sai kuma in ce: "Da sunan Allah muka shiga, kuma da sunan Allah muka fita, kuma ga Allah Ubangijin mu muka dogara".

3. Ina farawa da yin asuwaki, sannan in yi sallama ga masu gida.

Amsa: 1. Ina shiga ne da ƙafa ta ta hagu.

2. Sai in ce kafin shiga: "Da sunan Allah, Ya Allah lallai ni ina neman tsarin Ka daga shaiɗanu maza da shaiɗanu mata".

3. Ba na shiga da wani abun da yake akwai ambaton Allah acikin sa.

4. Ina ɓoyuwa a halin biyan buƙata.

5. Ba na magana a wurin da biyan buƙata.

6.Ba na fuskantar Al-ƙibla, kuma ba na juya mata baya, a yayin fitsari ko bayan gida.

7. Ina amfani da hannu na na hagu a kawar da najasa, ba na amfani da na dama.

8. Ba na biyan buƙata ta akan hanyar mutane ko kuma inuwar su.

9. Ina wanke hannu na bayan biyan buƙata.

10. Ina fita ne da ƙafa ta ta hagu, sai kuma in ce: "Ina neman gafarar Ka".

Amsa:1. Ina shiga masallaci ne da ƙafa ta ta dama, sai in ce: "Da Sunan Allah, Ya Allah Ka buɗa min ƙofofin rahamar Ka".

2. Ba na zama har sai na yi sallah raka'a biyu.

3. Ba na wuce wa ta gaban mai sallah, ko kuma in yi cigiyar ɓataccen abu acikin masallaci, ko in sayar ko kuma in saya a cikin masallaci.

4. Ina fita daga masallaci da ƙafa ta ta hagu, sai in ce: "Ya Allah, lallai ni ina roƙon Ka daga falalar Ka".

Amsa: 1. Alokacin da na haɗu da wani musulmi zan fara yi masa sallama, da faɗin: "Amincin Allah da rahamar Sa da kuma albarka Sa su tabbata a gare ku". ba da wanin sallama ba, bana nuni da hannu na shi kaɗai.

2. Ina yin murmushi a fuskar duk wanda nakewa sallama.

3. Kuma ina yin musafaha da shi da hannu na na dama.

4.Idan wani ɗaya ya gaishe ni da gaisuwa, to ni ma zan gaishe shi da mafi kyau daga gare ta, ko na mayar da tamkar ta.

5. Ba na fara yi wa kafiri sallama, idan ya yi sallama zan mayar masa da tamkar ta.

6. Kuma ƙarami yake fara yi wa babba sallama, wanda ke kan abin hawa shi zai fara yi wa mai tafiya a ƙasa sallama, wanda ke tafiya a ƙafa shi zai fara yi wa na zaune sallama, mutane kaɗan su za su fara yi wa masu yawa sallama.

Amsa: Ina neman izini kafin shiga wuri.

2. Ina neman izini sau uku, bana ƙarawa, bayan su sai in juya.

3, Ina ƙwanƙwasa kofa a hankali, ba na tsayawa a gaban ƙofa, kai a daman ta ne ko a hagun ta.

4. Ba na shiga ga baba na ko baba ta ko ɗaya daga ɗakunan kafin neman izini, musamman ma kafin Asuba, da lokacin baccin rana, da kuma bayan sallar Isha'i.

5. Zai iya yiwuwa na shiga wuraran da ba na zama ba, kamar: Asibiti, ko wurin kasuwanci ba tare da neman izini ba.

Amsa: 1. Ina ciyar da dabbobi kuma ina shayar da su.

2. Jin ƙai da tausayi ga dabbobi, da rashin ɗora musu abin da ba za su iya ba.

3. Ba na azabtar da dabbobi da kowanne irin nau'i na azaba, da cutarwa.

Amsa: 1. Ina niyyar samun ƙarfi saboda bautar Allah da kuma yardar Shi da motsa jiki.

2. Ba ma yin wasa a lokacin sallah.

3. Yara maza ba sa wasan motsa jiki tare yara mata.

4. Ina sanya kayan motsa jiki na wanda zai rufe mini al'aura ta.

5. Ina nisantar wasannin motsa jikin da aka haramta, kamar waɗanda acikin su akwai marin fuska, ko yaye al'aurori.

Amsa: 1.Gaskiya a kakaci da rashin ƙarya.

2. Kakaci wanda ya kaɗaita daga izgili da wulaƙanci da cutarwa da tsoratarwa.

3. Rashin yawaita kakaci.

Amsa: 1. Sanya hannu ko tufafi ko hankici yayin atishawa.

2. Ka godewa Allah bayan atishawa (ka ce): "Godiya ta tabbata ga Allah".

3. Sai ɗan'uwan sa ko abokin sa ya ce da shi: "Allah Ya yi maka rahama".

4. Idan ya faɗa masa: sai ya ce: "Allah Ya shiryar da ku, kuma Ya kyautata sha'anin ku".

Amsa: 1. Koƙari wurin matse hammar.

2. Rashin ɗaga murya da faɗin: "hah, ha".

3. Sanya hannu a baki.

Amsa: 1. Yin karatun da tsarki bayan alwala.

2. Zama da Ladabi da natsuwa.

3. Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗani a farkon karatu.

4. Ina jujjuya ma'anonin karatun.