BANGAREN HADISI

Amsa: An karɓo daga sarkin Muminai baban zaki Umar ɗan Khaɗɗabi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Kaɗai dukkan ayyuka basa tabbata sai da niyyoyi, kuma kowane mutum da irin niyyar da ya niyyata, wanda Hijirar sa ta kasance zuwa ga Allah da Manzon sa to Hijirar sa tana ga Allah da Manzon sa, kuma wanda Hijirar sa takasance dan duniya da zai same ta, ko wata mace da zai aure ta, to Hijirar sa tana ga abinda yayi Hijira zuwa gare shi. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

Abinda za'a iya koya daga Hadisin:

1. Kowanne aiki ba makawa gareshi daga niyya, na sallah, da Azumi da Hajji, da wasun su daga ayyuka.

2. Ba makawa daga tsarkakewa acikin niyya ga Allah - maɗaukakin sarki -.

Hadisi Na biyu:

Amsa: An karɓo daga Uwar muminai Babar Abdullahi A'isha - Allah ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - ya ce: "Wanda ya farar acikin al'amarin mu wannan abinda baya daga gare shi to shi abin juyarwane". Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

Abinda za'a iya koya daga Hadisin:

1. Hani daga ƙirƙira acikin addini.

2. Kuma fararrun ayyuka ababen juyarwa ne ba karɓaɓɓu bane.

Hadisi Na Uku:

Daga Umar ɗan Khaɗɗab - Allah ya yarda da shi - ya ce: “A yayin da muke zaune tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wata rana, yayin da wani mutum ya ɓullo mana, mai tsananin farin tufafi, mai tsananin baƙin gashi, ba a ganin alamun tafiya agare shi, kuma babu wani ɗaya daga cikin mu da ya san shi, har sai da ya zauna zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma ya sanya gwiwowin sa a gwiwoyin sa, ya sanya tafukan sa akan cinyoyin sa, sai ya ce: "Ya Muhammad, ka bani labari game da Musulunci? Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - ya ce: "Musulunci: Ka shaida cewa babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah, kuma lallai Muhammadu Manzon Allah ne, kuma ka tsayar da sallah, ka ba da zakka, ka Azumci Ramadan, kuma ka yi Hajjin ɗaki idan kasami ikon zuwa gare shi". Ya ce: "Ka yi gaskiya", sai mukayi mamakin sa, yana tambayar sa kuma yana gasgata shi. Yace: "To ka bani labari game da imani? Ya ce: "Ka bada gaskiya da Allah, da Mala'ikunsa, da littafan sa, da Manzannin sa, da Ranar Lahira, kuma ka yi imani da ƙaddara, alherin sa da sharrin sa. Ya ce: "Kayi gaskiya" Yace: "To kabani labari game da kyautatawa". Yace: "Ka bauta wa Allah kamar kana ganin sa, idan ka kasance ba ka ganin sa, to Shi yana ganin ka". Yace: "Ka bani labari game da Al-ƙiyama". Yace: "Wanda ake tambaya baifi wanda yake tambayar sani ba". Yace: "Ka bani labari game da alamomin ta". Yace: "Kuyanga ta haifi uwargijiyar ta, kuma kaga marasa takalma talakawa masu kiwon dabbobi, suna gasa acikin tsawaita gini'. Sannan ya tafi sai na zauna tsawon lokaci, sannan yace: "Ya Umar, shin kasan mai tambayar?" Na ce: "Allah da Manzonsa ne mafi sani" Yace: "Lallai shine Jibrilu, yazone dan ya sanar daku addinin ku". Muslim ne ya rawaito shi.

Abinda za'a iya koya daga Hadisin:

1. Ka ambaci rukunan Musulunci guda biyar, sune:

Shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Muhammadu Manzon Allah ne.

Da tsayar da sallah.

Da bayar da zakkah.

Da Azumin watan Ramadan.

Da Hajjin ɗakin Allah mai alfarma.

Ambaton rukunan Imani, su shida ne:

Imani da Allah.

Da Mala'ikun sa.

Da Littattafan sa.

Da Manzannin sa.

Da Ranar Lahira.

Da ƙaddara alherin sa da kuma sharrin sa.

3- Ambaton rukunan kyautatawa, shi rukuni ɗaya ne, shine, ka bauta wa Allah kamar kana ganin sa, idan ba ka kasance kana ganin sa ba to shi yana ganin ka.

4- Lokacin tashin Al-ƙiyama, babu wanda ya san shi sai Allah maɗaukakin sarki.

Hadisi na Huɗu:

Amsa: Daga Abu Huraira - Allah ya yarda dashi - yace: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mafi cikar muminai imani: Mafi cikar su a ɗabi'u". Tirmizine ya ruwaito shi kuma ya ce: "Hadisine kyakykyawa ingantacce".

Abinda za'a iya koya daga Hadisin:

1.Kwaɗaitarwa akan kyawawan halaye.

2. Kuma cikar ɗabi'u yana daga cikin cikar imani.

3. kuma cewa imani yana ƙaruwa kuma yana raguwa.

Hadisi na biyar:

Amsa: Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah ya yarda da su - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - ya ce: "Wanda ya rantse da wanin Allah, to haƙiƙa ya kafirta, ko ya yi shirka". Al-Tirmithi ne yawaito shi.

Abinda za'a iya koya daga Hadisin:

- Rantsuwa bata halatta sai da Allah - maɗaukakin sarki -.

- Rantsuwa da wanin Allah yana daga cikin ƙaramar shirka.

Hadisi na shida:

Amsa: Daga Anas - Allah ya yarda da shi - ya ce: Lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Dayan ku ba zaiyi imani ba har sai na kasance mafi soyuwa a gare shi daga mahaifin sa da ɗan sa da mutane baki ɗaya". Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

Daga cikin fa'idojin Hadisin:

-Son Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - yana wajaba sama da dukkanin mutane.

- Lallai hakan yana daga cikar imani.

Hadisi na bakwai:

Amsa; Daga Anas - Allah ya yarda da shi -, ya ce: Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Dayanku ba zaiyi imani ba har sai ya sowa ɗan uwan sa abin da yake sowa ga kan sa". Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

Daga cikin fa'idojin Hadisin:

1. Ya wajaba akan mumini yasowa muminai alheri kamar yadda yake sowa ga kan sa.

- Hakan kuma yana daga cikar imani.

Hadisi na Takwas:

Amsa: Daga Abu Sa'id - Allah ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Na rantse da wanda raina yake a hannunsa!, lallai cewa ita tayi daidai da ɗaya bisa ukun Al-ƙur'ani". Bukhari ne ya rawaito shi.

Daga cikin fa'idojin Hadisin:

1. Falalar Suratul Ikhlas.

2. Cewar ita tayi daidai da ɗaya bisa ukun Al-ƙur'ani.

Hadisi na Tara:

Amsa: Daga Abu Musa - Allah ya yarda da shi - yace: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Babu dabara kuma babu ƙarfi, taska ce daga cikin taskokin Aljanna". Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

Daga cikin fa'idojin Hadisin:

1. Falalar wannan kalmar, kuma ita taska ce daga cikin taskokin Aljanna.

2. Barrantar bawa daga dabarar sa da kuma ƙarfin sa, da dogaron sa ga Allah shi kaɗai.

Hadisi na Goma:

Amsa: Daga Nu'uman ɗan Bashir - Allah ya yarda dasu - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Ku saurara, kuma a cikin jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru, kuma idan ta ɓaci dukkan jiki ya ɓaci". Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

Daga cikin fa'idojin Hadisin:

1. Gyaran zuciya acikin sa akwai gyaran waje da ciki.

2.Himmatuwa akan gyaran zuciya, domin akwai gyaruwar mutum da shi.

Hadisi na goma sha ɗaya:

Amsa: Daga Mu'azu ɗan Jabal - Allah ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ƙarshen zancen sa ya kasance babu abin bautawa da gaskiya sai Allah zai shiga Aljanna". Abu Daud ya ruwaito shi.

Daga fa'idojin Hadisin:

1. Falalar : Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma bawa zai shiga Aljanna da ita.

2. Da falalar wanda ƙarshen zancen sa na duniya yakasance Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah.

Hadisi na sha biyu:

Amsa: Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mumini bai zama mai yawan sukar mutane ba, kuma ba mai yawan tsinuwa bane, kuma ba mai alfasha bane, kuma ba mai yawan batsa bane". Al-Tirmithi ya ruwaito shi.

Daga cikin fa'idojin Hadisin:

1. Hani daga ɓatacciyar magana da mummuna.

2. Lallai cewa wannan siffar mumini ce a harshen sa.

Hadisi na sha uku:

Amsa: Daga Abu Huraira - Allah ya yarda dashi - yace: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Yana daga kyawun Musuluncin mutum, barin sa abin da babu ruwan sa". Tirmizi ne ya ruwaito shi da wanin sa.

Daga cikin fa'idojin Hadisin:

1. Barin abinda bai shafi mutum ba, na daga al'amuran addinin wanin sa da kuma duniyar sa.

2. Lalle barin abin da bai shafi mutum ba to yana daga cikar Musuluncin sa.

Hadisi na Sha Huɗu:

Amsa: Daga Abdullahi ɗan Mas'ud: Lalle cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - ya ce: "Wanda ya karanta wani harafi daga littafin Allah to yana da kyakykyawan lada, kuma kowane lada za'a ninkashi da tamkarsa goma, bazance: Alif lam meem harafi ɗaya bane, sai dai Ali harafi ne, Meem harafi ne". Al-Tirmithi ya ruwaito shi.

Daga cikin fa'idojin Hadisin:

1. Falalar karanta Al-ƙur'ani.

2. Kuma akan kowanne harafi da ka karanta kana da kyawawan lada da shi.