BANGARAN TARIHIN ANNABI (TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA AGARESHI).

Amsa: Shi ne Muhammad ɗan Abdullahi ɗan Abdulmuɗallabi ɗan Hashim. Shi Hashim daga Kuraishawa yake, su kuma Kuraishawa daga Larabawa suke, su kuma Larabawa daga zuriyar Annabi Isma'il suke, Isma'il kuma ɗan Annabi Ibrahim - tsira da amincin Allah su agareshi - da kuma Annabin mu.

Amsa: Sunanta Amina 'yar Wahab.

Amsa; Babansa ya rasu ne a Madina alhali shi yana ciki, ba'a ma haifeshi ba - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -.

Amsa: A shekarar giwa, ranar Litinin daga watan Rabi'ul Awwal.

Amsa: A cikin Makkah.

Amsa: Baiwar babansa Ummu Aiman.

- Baiwar babbanfansa Abu Lahab, Suwaiba.

- Haimat Al-Sa'adiyya.

Amsa: Babar shi ta rasune alhali shi yana ɗan shekara shida, sai kakan sa Abdulmuɗallabi ya reneshi.

Amsa: Kakansa Abdulmuɗallabi ya rasu alhali shi yana da shekara takwas, sai baffansa Abu Dalib ya reneshi.

Amsa: Yayi tafiya tare da baffansa zuwa Sham alhali shekarunsa shekara goma sha biyu ne.

Amsa: Tafiyar sa ta biyu ta kasance ne ta fatauci da dukiyar Nana Khadija - Allah ya yarda da ita -, yayin da ya dawo sai ya aureta - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -, alhali yana da shekaru ashirin da biyar.

Amsa: Kuraishawa sun sake gina Ka'aba ne a lokacin yana da shekara talatin da biyar.

Sai suka sa shi mai yanke hukunci a tsakanin su yayin da suka yi saɓani akan wa zai sanya baƙin dutse, sai ya sanya shi a wani tufafi, ya kuma umarci kowacce ƙabila ta kama gefen tufafin, sun kasance ƙabilu huɗu, da suka ɗaga shi zuwa bigirensa, sai - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya sanya shi da hannunsa.

Amsa: Shekarunsa sun kasance Arba'in ne kuma an aikoshi ne zuwa ga mutane baki ɗaya mai bushara kuma mai gargaɗi.

Amsa: Mafarki na gaskiya, ya kasance ba ya ganin mafarki face ya zo kamar ɓullowar Asuba.

Amsa: Ya kasance yana bauta wa Allah a kogan Hira, kuma yana yin guzuri saboda hakan.

Kuma wahayi ya sauka a gare shi, alhali yana kogon Hira yana bauta wa Allah.

Amsa: Faɗin Allah -maɗaukakin sarki -: {Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda yayi halitta 1. Ya halicci mutum daga gudan jini 2. Ka yi karatu, kuma Ubangijinka shine mafi girma 3. Wanda Ya sanar (da mutum) da alƙalami 4. Ya sanar da mutum abin da bai sani ba}. [Surat Al-alaq: 1-5].

Amsa: Daga cikin maza: Abubakar Siddiƙ, daga cikin mata: Nana Khadija 'yar Khuwailid, daga cikin yara: Aliyu ɗan Abu Dalib, daga cikin 'yantattu: Zaidu ɗan Harisah,daga cikin bayi: Bilal ɗan Rabah, da Allah ya yarda da su da wasunsu.

Amsa: Da'awar ta kasance ne a ɓoye wajen shekaru uku, sannan sai Ma'aikin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - yayi umarnin bayyanar da Da'awar.

Amsa: Mushirikai sun kai matuƙa wurin cutar dashi da cutar da musulmai, har sai da yayi izini ga muminai da Hijira zuwa wurin Najashi a Habasha.

Ma abota shirka suka haɗu akan cutarwa da kuma kashe Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -, sai Allah ya tsare shi, ya kewaye shi da baffansa Abu Dalib domin ya tsare shi daga garesu.

Amsa: Baffansa Abu Dalib ya rasu, da kuma mai ɗakinsa Nana Khadija - Allah ya yarda da ita -.

Amsa: Hakan ya kasance ne a shekaru hamsin daga rayuwarsa, kuma aka wajabta masa salloli biyar.

Isra'i: Shi ne tafiya daga Masallaci mai alfarma zuwa Masallaci mafi nisa (Kudus).

Mi'iraji: Ya kasance ne daga Masallaci mafi nisa (Kudus) zuwa sama har zuwa magaryar tuƙewa.

Amsa: Ya kasance yana kiran mutanan Da'ifa, kuma yana zuwa wuraran taruka da matattarar mutane, har mutanan Madina daga cikin Ansar sukazo, suka yi imani da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - kuma suka yi masa caffa akan taimaka masa.

Amsa: Ya wanzu ne tsawon shekara goma sha uku.

Amsa: Daga Makkah zuwa Madina.

Amsa: Shekaru goma.

Amsa: An wajabta masa Zakka, da Azumi da Hajji, da Jihadi, da kiran sallah, da wasunsu na Shari'o'in musulunci.

Amsa: Babban yaƙin Badar.

Yaƙin Uhud.

Yaƙin Taron dangi.

Yakin Buɗe Makka.

Amsa: Faɗinsa - maɗaukakin sarki -: {Kuma ku ji tsõron wani yini wanda ake mayar da ku a cikinsa zuwa ga Allah, sa'an nan kuma a cika wa kõwane rai abin da ya sanã'anta, kuma sũ bã a zãluntar su 281}. [Surat Al-Baƙarah: 281].

Amsa: Ya rasu a watan Rabi'ul Awwal, a shekara ta goma sha ɗaya daga Hijira, yana da shekaru sittin da uku.

Amsa: 1. Nana Khadija 'yar Khuwailid -Allah ya yarda da ita -.

2. Nana Saudatu 'yar Zam'ah - Allah ya yarda da ita -.

3. Nana A'isha 'yar Abubakr - Allah ya yarda da ita-.

4. Nana Hafsatu 'yar Umar - Allah ya yarda da ita -.

5. Nana Zainab 'yar Khuzaimah - Allah ya yarda da ita -.

6. Ummu Salamah Hindu 'yar Abu Umayya - Allah ya yarda da ita -.

7. Ummu Habiba Ramlatu 'yar Abu Sufyan - Allah ya yarda da ita -.

8. Juwairiyya 'yar Haris - Allah ya yarda da ita -.

9. Maimuna 'yar Haris - Allah ya yarda da ita -.

1.Safiyya 'yar Hayayi - Allah ya yarda da ita -.

11. Zainab 'yar Jahash - Allah ya yarda da ita -.

Amsa: Daga cikin maza akwai uku:

1.Alƙasim, da shi yakasance ake masa alkunya.

Da Abdullahi.

Da Ibrahim.

Daga mata kuma akwai:

Fatima.

Ruƙayyah.

Ummu Kulsum.

Zainab.

Dukkanin 'ya'yansa daga Nana Khadija ne - Allah ya yarda da ita - in banda Ibrahim, kuma dukkanin su sun rasu kafin sa in banda Fatima, ta rasu bayan sa da watanni shida.

Amsa: Ma'aikin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance tsaka tsaki ne cikin mutane, ba gajere bane kuma ba dogo bane, kai ya kasance tsakanin haka, ya kasance fari ne da sirkin ja - tsira da aminci su tabbata a gare shi - ya kasance mai kaurin gemu ne, mai yalwatattun idanuwa, mai yalwataccan baki, gashinsa mai tsananin baƙi ne, mai faɗin kafaɗu ne, mai daɗin ƙanshi ne, da wanin haka na kyakykyawar halittarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi -.

Amsa: Ya bar al'ummar sa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - akan hanya fara ƙal, daranta kamar hantsinta, babu wanda yake karkata daga gareta sai halakakke, babu wani alheri da ya bari face sai da ya shiryar da al'umma a kansa, haka kuma babu wani sharri sai da ya tsoratar da ita daga gareshi.